An gurfanar da ƴansandan Kenya biyar kan tserewar ƙasurgumin mai kisan mata

Spread the love

An gurfanar da jami’an ƴansandan Kenya biyar bisa zargin taimaka wa mutumin da ake zargi da kashe mata da dama tserewa, har ma da wasu ƴan ƙasar Eritiriya 12 da ake zargi da laifin shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba.

Masu gabatar da ƙara sun buƙaci ƙarin kwanaki goma 14 su ci gaba da tsare su domin gudanar da bincike.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata lokacin da Collins Jumaisi Khalusa, wanda rahotanni suka ce ya amsa laifin kashe mata 42 ciki har da matarsa, ya tsere daga inda ake tsare da shi.

Manyan jami’ai sun ce sun yi imanin cewa akwai haɗin baki tsakanin jami’an ƴansandan.

Khalusa, mai shekara 33 a duniya, an tsare shi ne da farko bayan da aka tsinci gawarwak a wata bola a birnin Nairobi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *