Babbar kotun shari’ar addinin musulinci ta Kasuwa dake zaman ta, a Shawuci Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Mallam Abdu Abdullahi Wayya, ta bayar umarnin tsare wata budurwa, mai siyar da Awara bisa zarginta da samar da mummunan rauni ga wani matashi ta hanyar watsa masa man suyar Awarar a jikinsa.
Ana tuhumar Ummussalam Alkasim, ta yi amfani da man suyar Awarar, inda ta watsawa masa, wai saboda ya na cin awararta amma baya biyan kudin.
Lauyar gwamnatin jahar Kano, Barista Amina Yahaya , ita ce ta gabatar da takaddar tuhumar kuma ta roki kotun da aka karanto kunshin tuhumar da ake yi wa matashiyar budurwar, sai dai bayan an karanto mata ta musanta zargin.
Amma dai ta shaida wa kotun cewa matashin, zuwa yake yi yana ci mata Awara ba tare da ya biya kudin ba, shi yasa ta dauki wannan mataki.
Alkalin kotun mai shari’a Abdu Abdullahi Wayya, ya bayar umarnin tsare ta, a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya har zuwa ranar 8 ga watan Oktoba 2024, don gabatar da shaidu.
Idongari.ng, ta ruwaito cewa ana tsaka da gudanar da shari’ar, aka kama wani da ake zargi da fakewa da shari’a don ya saci baburan al’umma.
An kama wanda ake zargin ne a lokacin da ya bude wani babur yake kokarin guduwa, inda aka mikashi hannun jami’an yan sanda don gudnaar da bincike.
- Bobrisky: Majalisar Wakilai Za Ta Binciki Zargin Almundahanar Da Ake Yiwa EFCC, NCS
- Gwamnatin Najeriya ta dakatar da manyan jami’an gidan yari kan zargin rashawa