An Gurfanar Da Dattijo Da ’Ya’yansa Biyu Bisa Zargin Sayar Da Kayan Maye A Kano

Spread the love

Al’umma a Tamburawar Yamma da Unguwar Makera a Karamar Hukumar Dawakin Kudu da ke jihar Kano, sun kai ƙara kan wani dattijo mai kimaninm shekara 72 tare da ’ya’yansa biyu, ciki har da wata budurwa, bisa zargin sayar da kayan maye, musamman madarar sukudaye.

Jagoran al’ummar, Dagacin Tamburawar Dan-Tube, Alhaji Auwalu Umar ne ya jagoranci kai karar.

An gurfanar da su a gaban Kotun Majistare mai lamba 28 da ke Gano, ƙarƙashin Mai Shari’a Hajiya Malika Muhammad.

Masu ƙarar sun ce rikicin ya samo asali ne bayan shugaban ƙungiyar tsaro ta unguwa ya nemi dattijon ya daina sayar da kayan maye, abin da daga bisani ya haifar da bore daga ’ya’yansa, inda ɗaya daga cikin ’yan kwamiti ya ji rauni.

’Yan sanda sun damke wadanda ake zargi bayan samun rahoton al’umma, inda aka gurfanar da su a kotu bisa tuhumar haɗa baki, tsoratarwa da mallakar kayan maye.

Bayan gabatar da ƙara, jami’in ’yan sanda, Insfekta Fago Lalon, ya karanta tuhumar, sai dai daga baya dangin wadanda ake zargi sun nemi a sasanta da wadanda abin ya shafa.

Kotun ta amince da ba da su beli, tare da gindaya sharuɗɗan da suka haɗa da kawo dattijon mai shekara 72 a kowane zama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *