An Gurfanar da Daya Daga Cikin Wadanda Ake Zargi Da Kashe Dan Sanda A Kano.

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar kano, ta gurfanar da daya daga cikin matasan da ake zargi da kashe wani dan sanda, mai suna Murtala Auwalu, a kan titin france road lokacin da yake tsaka da gudanar aiki, a ranar 1 ga watan Janairun 2025.

An gurfanar da Abdussalam Lawan, gaban kotun Majistiri dake zaman ta a unguwar Gyadi-gyadi Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Haulatu Magaji, da tuhumar hada kai don aikata laifi da kuma kisan kai , wanda yain hakan ya saba da sashi na 221 amma ya musanta zargin da ake yi masa.

Tunda fari ana tuhumar matashin da kuma wasu abokansa wadanda suka gudu, da hannu dumu-dumu wajen kashe jami’in dan sandan.

Alkaliyar kotun mai shari’a Haulatu Magaji , ta dage ci gaban sauraren shari’ar zuwa ranar 11 ga watan Fabarairun 2025, don samun shawarwarin gwamnati sakamakon rashin hurumin kotun.
Daga daga cikin matan jami’in dan sandan da aka halaka ta yi kira ga sarkin Kano, Gwamnan Kano da kwamishinan yan sanda su kara fadada binciken kan wanda ake zargin domin yi mu su adalci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *