A Kenya an gurafar da wani fasto kan zargin kisan kai, bayan da aka gano gawawwaki sama da 400 da aka binne a wani rami mai zurfi a wani jeji da ke gabashin kasar.
Wasu daga cikin waɗanda suka tsira da ƴan’uwan waɗanda suka mutu, sun ce Paul Mackenzie ya nemi mabiya cocinsa da yin azumi domin “haɗuwa da Yesu”.
Sai dai shi da wasu mutum 29, sun musanta aikata lafin da ake tuhumar su da aikatawa a lokacin zaman kotun da aka yi a birnin Malindi.
Tuni aka tuhumi Mackenzie da aikata laifukan ta’addanci, da azabtar da yara ƙanana, wani zargi da ya musanta aikatawa.
Ƴansanda da lauya mai gabatar da ƙara sun yi zargin cewar baya ga yunwa, wasu daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su, an shaƙe su, sannan aka toshe musu hanyoyin shaƙar isa, ko aka yi ta dukan su har suka mutu.
Ana zargin mutum 30 ɗin da laifin kisan mutum 191.
Muna son a yi sasanci kan ficewar kasashen Sahel daga Ecowas – Yan farar hula
‘Kaso 30 na mace-macen Jarirai a Duniya na faruwa ne a Najeriya
“Har yanzu ina jin tsoron sa”, ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira ta shaida wa BBC, a lokacin da aka aka tambaye ta abin da za ta faɗa wa Mackaenzie idan har ta gamu da shi.
“Ba na son ganin shi ko kaɗan,” in ji matar mai shekara 29 a duniya, wadda ke da yara huɗu.
Neema wanda ba sunanta na gaskiya ke nan ba, ta kasance mai bin cocin Good News International da ke Minlindi har zuwa lokacin da aka rufe shi a 2019.