An gurfanar da Kwastoma bayan ya sace Kudin da ya biya Karuwa.

Spread the love

An gurfanar da wani matashi a gaban kotu bisa zargin sace kudin da ya biya wata mace mai zaman kanta da ya yi lalata da ita.

Dan sanda mai gabatar da kara, Salewa Ahmed, ya shaida wa kotun da ke zamanta a Ibadan, Jihar Oyo, cewa matar ce ta kai kara cewa matashin mai shekaru 28 ya sace N3,000 da ya biya ta da kuma wayarta.

Salewa Ahmed, ya sanar da kotun da ke zamanta a Ibadan, jihar Oyo, cewa wanda ake zargin an kama shi ne bayan matar ta kai rahoto a caji ofis na Idi-Aro cewa kwastoman nata ya damfare ta.

Dan sandan ya shaida wa alkali cewa bayan sun gama lalata ne matashin ya biya ta kudin da suka amince a ranar 19 ga watan Janairu, amma ya faki idonta ya koma dakin ya sace kudin da kuma wayarta da kudinta ya kai N46,000.

karan ta wannan labarin Tinubu na duba yiwuwar kafa ‘yan sandan jihohi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *