An gurfanar da wani magidanci a gaban kotun shari’ar addinin musulinci, dake zamanta a hukumar Hisbah ta jahar Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Sani Tamin Sani Hausawa, bisa zarginsa da lakada wa matarsa duka,har sai da jaririn da ya ke bayan ta ya fado kasa.
Mai gabatar da kara na kotun, ya karanto masa kunshin tuhumar gwada karfi, amma ya musanta zargin.
Matar magidancin ta shaida wa alkalin kotun cewar ta yafe wa majin na ta.
Tunda fari sun samu sabani na rashin fahimtar juna , wanda ya kai ga magidancin ya baiyana fushin a fili ta hanyar lakadawa matarsa duka, har sai da makota suka kawo mata dauki.
- Rundunar Yan sandan Kano Ta Bukaci Al’umma Su Nuna Kishin Kasa Da Zaman Lafiya Gabanin Hukuncin Babbar Kotun Tarayya
- Kotu Ta Hana Belin Abba Kyari.