Babbar kotun shari’ar addinin musulinci, dake zaman ta a garin Bichi Kano, ta bayar da umarnin tsare wani matashi mai suna Awaisu Ibrahim, bisa zarginsa da aikata laifin shiga ta laifi, tsoratarwa da kuma.
Mai gabatar da kara na kotu Corporal Imrana Lawan, ya karanto masa kunshin tuhumar da ake yi masa inda nan ta ke ya amsa laifinsa.
Idongari.ng, ta ruwaito cewa ana zargin matashin da shiga gidan wata matar aure da misalin karfe 2 na dare, tare da makami inda ya tsoratar da ita da kuma karbe mata wayar hannu.
Mai gabatar da karar ya roki kotun ta kafa masa shaidun jin ikirari da karawa wanda ake zargin tuhumar fashi da makami, saboda ya shiga da makami gidan mutane karkashin sashi, 223 na kundin ACGL 2019.
Kotun ta karbi rokon mai gabatar da karar , tare da karanta masa sabuwar tuhumar fashi da makami, kuma nan ta ke ya amsa.
Alkalin kotun mai shari’a Mallam Kabiru Idris Sadik Fagge, ya kafa masa shaidun jin ikirari tare da bayar da umarnin tsare shi a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya.
- Kotu ta bayar da sammacin kama ɗan Birtaniya kan yunƙurin kifar da gwamnatin Tinubu
- Tinubu Ya Saba Yarjejeniyar Da Muka Yi da shi kan ƙara farashin fetur – NLC