Wata kotun majistiri dake zaman ta, a Kano ta bayar da umarnin tsare matasan da ake zargi da yin garkuwa da Wani karamin yaro, Dan Shekaru hudu a duniya, har suka Nemi kudin fansar naira Miliyan 10.
An karanto wa matasan kunshin tuhumar hadin baki , aikata laifi da kuma yin garkuwa da mutane, amma sun musanta zargin.
Wadanda ake zargin sun hada da Hisbullah Salisu mai Shekaru 30 da Hassan Ali Rabi’u mai Shekaru 28 dukkaninsu mazaunan unguwar Yakasai, sai kuma Hassan Ali mai Shekaru 22 mazaunin unguwar Hotoro Kano.
Tunda fari yan sandan kano ne suka kama su , sannan suka gurfanar da su a gaban kotun, bisa zargin yin garkuwa da karamin yaro mai suna Muhammed Nasir Jamilu, mazaunin Sharada Kano, a ranar 7 ga watan Satumba 2024, Inda suka Kai shi karamar hukumar Gwarzo Kano, har suka karbi kudin fansar naira miliyan 1o, amsa sun karbi naira Dubu dari Uku, Kafin a cika mu su ragowar kudin.
Kotun karkashin jagorancin mai shari’a Rakiya Lami Sani, ta aike da su zuwa gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya har zuwa ranar 30 ga watan Oktabo 2024.
- Zaɓen Edo: An rufe rumfunan zaɓe bayan kammala kaɗa ƙuri’a
- An Cafke Mutumin Da Ake Zargi Da Kai Wa Yan Bindiga Makamai