An Gurfanar Da Wani Mutum Da Kunshin Takaddun Tuhuma 8 A Kano.

Spread the love

An gurfanar da wani Mutum mai suna, Usman Sunusi Bachirawa, a gaban kotun majistiri, dake zamanta a unguwar gyadi-gyadi Kano da kunsin takaddun tuhuma har guda 8.

Jami’in kotun Aminu Kurawa, ya karanto masa kunshin tuhumar zamba da cuta, inda ake zargin ya karbi kudi naira miliyan daya a wajen Bashir Hassan da Usaini Hassan, don ya kai su kasa mai tsarki amma ya basu takaddar Visa ta bogi.

Idongari.ng, ta ruwaito cewa, lauyan wanda ake zargin barista A.I. Alhassan ya roki kotun ta bayar beli, kuma ta amince tare da sanya sharadin zai kawo mutane 2, da suka hada dan uwansa da kuma mamallakin kamfanin zirga-zirga tare da ajiye naira dubu dari 800.

DANDALIN KANO FESTIVAL

Haka zalika an kara karanto masa kunshin tuhumar takaddun karar da Aminu Dayyabu ya shigar, inda ake zargin Usman Sunusi Bachirawa, ya karbar masa naira  dubu dari shida da saba’in, sai kudin Salman Inusa Naira dubu dari 300 da kudin Mujahid Abdullahi naira dubu dari 570 sannan ana zargin ya karbi kudin Yusuf Adamu har naira dubu dari 600.

Bayan karanto masa kunshin tuhume-tuhumen ya musanta, inda lauyansa ya roki kotun ta bayar da belinsa.

Alkaliyar kotun mai shari’a Rakiya Lami Sani, ta sanya shi a hannun beli, bisa sharadin farko tare dage ci gaabn shari’ar zuwa ranar 21 ga watan Oktoba 2024.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *