An gurfanar da wasu matasa a gaban kotun musulnci bisa zargin dukan wani mutum kan takaddamar siyan ruwa.

Spread the love

 

An gurfanar da wasu matasa a gaban kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta a unguwar Gama PRP Kano, bisa zargin su da hada kai da kuma samar da rauni , wanda laifin ya saba da sashi na 120 da 158 na kundin Penal code.

Matasan da ake zargi sun hada da Sani Muhammad dPa kuma Huzaifa Sani da suka hada kan suka yi wa Umar Muhammad Larabar Abasawa dukan tsiya , har suka jefa shi cikin kwata wanda shi ne sanadiyar samun raunin da yayi.

Kotun ƙoli ta tabbatar da hukuncin daurin shekara 5 kan Farouk Lawan

Tunda fari , wanda aka jiya raunin ya tsayar da mai kurar ruwa domin ya siya, sai kawai matasan suka ce, lallai fa wannan mai kurar ruwan gidansu zai kai , sai dai Umar Larabar Abasawa ya shaida mu su cewar, shi ne ya taro mai kurar ruwan tun daga titin har zuwa cikin lungu , nan fa sa’insa ta kaure a tsakanin suka yi masa duka tare da jefa shi cikin kwata.

kan hakan ne ya sanya shi garzaya wa wajen jami’an yan sanda ya gabatar da korafin sa , inda su kuma suka gurfanar da su a gaban kotun shari’ar addinin musulincin dake Gama PRP.

Wasannin da za su fi zafi a zagayen ƴan 16 na gasar Afcon 2023

Mai gabatar da kara Aliyu Abidin Murtala , ya karanto musu kunshin tuhumar da ake yi musu ne , sai dai kotun ta bayar da umarnin tsare su a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya har zuwa ranar 13 ga watan December 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *