An gurfanar da wata mata mai suna A’isha Ibrahim Hadejia, mai shekaru 38 a duniya, wadda ake tuhuma da wasu mutane biyu Alhaji Tijjani Garba da kuma Alhaji Haruna, wadanda basa gaban kotun da laifin hada baki, zamba cikin aminci da kuma cin amana.
Laifin da ake zarginsu da aikata wa ya saba da sashi na 120, 203 da 206 na kundin SPCL.
Idongari.ng, ya ruwaito cewa tun a shekarar 2022 , wadda ake tuhuma ta farko A’isha Ibrahim, ta hada kai da Alhaji Tijjani Garba da Alhaji Haruna, inda suka damfari masu kara da suka hada da Hamza Abubakar da Muhammed Abubakar mazauna unguwar Dantamashe Kano, ta hanyar karbar kudi a wajen su har naira Miliyan tamanin da dubu dari da saba’in da biyar da zummar za a kawo mu su kayan abinci, kamar shinkafa,Gero, Masara bayan an girbe amfanin Gona.
Masu karar sun bayyana cewar sun ba su kudin, amma tunda daga karbar kudaden suka yi hafzi da su tare da kashe wayoyinsu aka rasa su.
Mai gabatar da kara Aliyu Abidin Murtala, ya karanto mata kunshin tuhumar da ake yi mata , inda nan ta ke ta musanta zargin.
Lauyan dake kare wadda ake tuhuma ya roki kotun ta bayar da belin wadda ake tuhumar, inda kotun ta waiwayi masu kara don ji daga gare su.
Sai dai mai gabatar da karar ya roki kotun ta basu dama zuwa ranar Laraba dan yin martani a rubuce.
Mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmed, ya bada umarnin tsare wadda ake zargin a gidan a jiya da gyaran hali da tarbiya.