An Guurfanar Da Matasan Da Ake Zargi Da Yin Garkuwa Da Kisan Kai A Kano.

Spread the love

Kotun Majistiri mai lamba 4, dake zaman ta a jahar Kano, ta aike wasu matasa yan uwan juna, zuwa gidan ajiya da gyaran da tarbiya, bisa zarginsu da aikata laifin garkuwa da kuma kisan kai.

Matasan da ake zargin sun hada, Musa Usman da kuma Abdullahi Usman, wadanda ake zargin da hada baki don aikata laifi, boye gaskiya, Yin garkuwa da kuma kisan kai.

Bayan gurfanar da su ne jami’in kotun, Aminu Kurawa , ya karanto mu su kunshin tuhume-tuhumen da ake yi, inda suka musanta zarge-zargen, duk da cewar kotun bata da hurimin sauraron shari’ar.

Jaridar idongari.ng, ta ruwaito mu ku cewa, ana zargin su da yin garkuwa da wani Yaro Mai suna Abdullahi Sani Hotoron Fulani, har ake zargin sun hallaka shi tare da jefa gawarsa sa cikin Masai irin ta zamani.

Tun ranar 15 ga watan Fabarairun 2024, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane uku bisa zargin garkuwa da wani yaro.

Cikin sanarwa da kakakin rundunar yan sandan jahar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar , ta ce a ranar 8 ga watan Fabrairu ne, ta samu rahoto daga wani mutum mai suna Alhaji Rabi’u Abdullahi da ke unguwar Hotoron Fulani cewa wasu mutane sun sace dansa mai suna Abdullahi Sani, inda suka bukaci ya biya naira miliyan hudu don sakin dan nasa.

Sanarwar ta ce daga nan ne kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Muhammed Usaini Gumel , ya umarci sashen yaki da garkuwa da mutane na rundunar ‘yan sandan jihar su tabbatar da kubutar da yaron tare da kama wadanda ake zargin.

Binciken ‘yan sanda ya kai ga kama wasu mutum biyu a unguwar Hotoron Fulanin da suka dage wajen daidaitawa kan kudin fansar da wadanda suka saci yaron.

Mai shari’a Rakiya Lami Sani, ta bayar da umarnin tsare su a gidan a jiya da gyaran hali da tarbiya har zuwa ranar 5 ga watan Yuni 2024.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *