Biyo bayan korafe-korafen da al’umma ke yi a kan shirya fina-finan dake nuna fadan Daba da harkar yan Daudu, a jahar Kano Shugaban Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta jahar Kano, Abba El-mustapha ya bada umarnin dakatar wa tare da hana dukkan fina-finan dake nuna fadan daba da harkar Daudu a fadin jahar Kano.
Abba El-mustapha na bada wannan umarni ne a yau, jim kadan bayan wata ganawa da ya yi da manyan ma’aikatan Hukumar tace fina-finan na Kano tare da wasu daga cikin wakilan yan masana’antar shirya fina-finan ta kannywood wanda suka hada da kungiyoyin MOPPAN, AREWA FILMS MAKERS DIRECTORS da kuma PRODUCERS.
- Tinubu ya sa hannu kan dokar bai wa ɗalibai bashin karatu
- Matatar Dangote Ta Soma Sayar Da Man Dizel Da Na Jirgin Sama
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar tace Fina-Finai Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar
Haka zalika Abba ya kara da cewa doka ce ta bawa Hukumar damar dakatarwa ko hana duk wani film da ta ke ganin yaci karo da tarbiya tare da al’adar al’ummar dake jahar, a saboda haka tuni lokaci ya shige da za’a saka ido irin wannan gurbatattun fina-finai su ci gaba da yaduwa a cikin al’umma.