An Haramta Wa Kafafen Yada Labarai Tattauna Batun Rashin Lafiyar Poul Biya A Kamaru.

Spread the love

Gwamnatin kasar Kamaru ta haramta wa kafafen yada labarai tattauna wa batun rashin lafiyar shugaban kasar Paul Biya.

Tun a watan satumba 2024, aka daina ganin duriyar Poul Biya mai shekaru 91 a duniya, abinda ya kara haifar da zazzafar muhawa a tsakanin yan kasar ga me da rashin lafiyar da yake fama da ita.

Biya, ya hau kan karagar mulki tun a ranar 6 ga watan Nuwamban 1982, kuma shi ne shugaban kasa  mafi dadewa a nahiyar Afrika, kuma na biyu  mafi tsufan shugaban kasa a duniya.

Gwamnatin ta bayyana dakatar da kafafen yada labaran ne a wata sanarwa da ta fitar mai kwanan watan 9 ga watan Oktoba 2024, mai dauke da sa hannun ministan cikin gida,Paul Atanga Nji.

Tuni dai aka aike da takardar ga gwamnonin Kamarun baki daya, inda ta umarci kafafen yada labarai ma su zaman kansu da kuma shafukan sada zumunta da su kaurace wa tattauna batun rashin lafiyar Poul Biya..

Ministan ya kara da cewa Poul , shi ne shugaban kasa don haka tattauna halin da yake ciki lamari ne da ya shafi tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *