An Kaddamar Da Dakarun Yan Sanda Na Musamman Don Bayar Da Tsaro A Makarantun Kano.

Spread the love

Rundunar Yan Sandan Jahar Kano, ta kaddamar da Dakarun yan sanda 60, wadanda za su zagaya don gano makarantun da za a kaiwa hari don inganta tsaronsu.

Kwamishinan Yan Sandan Jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, ne ya bayyana hakan a wani bangare na bikin cikarsa shekara guda a matsayin Kwamishinan Yan Sandan Jahar.

CP Muhammed Gumel, ya ce Babban sufeton Yan Sandan Nigeria, IGP Kayode Adeolu Abegketun, ya bayar da umarnin sakamakon farmakin da ake kaiwa makarantun, Primary, Secondary da kuma na manyan makarantu, a wasu yankunan Kasar hakan ne ya sanya suka zabi jajirtattun yan sanda 60 har aka ba su horo a birnin tarayya Abuja.


CP Gumel, ya Kara da cewa akwai ma su Neman bayanan sirri wadanda za su ci gaba da kewaya wa, domin zakulo maganganu da suke yin barazana ga Wata Makaranta, musamman yadda mahara ke Kai hari don daukar yara a makarantu Kafin su nemi kudin fansa.

Kwamishinan Yan Sandan ya ce harkar Ilimi harkar ilimi harka ce Babba , kuma Rundunar Yan Sanda ba za ta yi wasa da ita ba.

“Wannan ya nuna cewa za mu Kama aiki Hayhata-Hayhata”

Dakarun dai an ba su horo a Abuja kan yadda za su tabbatar sun kare Kansu , da kuma kare Daliban Makarantu.

Haka zalika an horas da dakarun kan yadda Yan ta’adda suke Shirya Kansu , su kawo hari ba tare da angane ba , inda ya ce an horas da su dabarun gano hakan.

Ya Kara da cewa, shi ne tsarin da Babban sufeton Yan Sandan Nigeria, ya bayar kuma shi suka gabatar, don bayar da gudunmawar da ta dace a bangaren ilimin Kano.

Ya yi Kira ga al’ummar jahar Kano, da su ba wa dakarun Rundunar hadin Kai , tare da Kara yin Kira ga gwamnati da kamfanoni da su ci gaba da taimakawa wajen samun nasarar dakarun.

Tuni dai kamfanin Hypo, ya kawo gudunmawarsa don taimakawa ta Stand domin zaman Yan sanda a lokacin da ake Rana ko ruwa domin tsallakar da yara zuwa makarantu.

Haka zalika an kaddamar Mujallar Rundunar Yan jahar Kano, wadda ta kunshi aiyuka da kuma nasarorin Rundunar Yan Sandan da aka samu cikin shekara daya, karkashin jagorancin Kwamishinan Yan Sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *