An Kaddamar Da Gidauniyar Muhammad Bashir Lamido Reshen Jahar Kaduna.

Spread the love

An KaddamarDa Gidauniyar  Muhammad Bashir Lamido Reshen Jahar Kaduna.

Da yake kaddamar da gidauniyar a Kaduna Shugaban gidauniyar shiyyar Arewa Maso yammacin kasar nan Abdullahi Isah ya godewa mambobin wannan Gidauniya reshen jihar Kaduna saboda samun lokacin hallartan wannan taro, yace hakan ya nuna Kaunan su ga Muhammad Bashir lamido da kuma kaunar tafiyar da mutane masu hangen nesa.

Har ila yau kaddamar da wanan Gidauniya Abdullahi Isah ya ce hakan ya nuna nasarar fara wannan tafiya domin cigaban al’ummar Nigeria.

Ya ce kadan daga Manufofin wannan Gidauniya ta Muhammad Bashir lamido shi ne don samar da cigaba mai ma’ana wacce zata taimaka wajen ci gaban Al’ummar kasar nan baki daya.

Abdullahi Isah ya ce Muhammad Bashir lamido mutum ne da ya yi shura wajen taimakawa mutanen a bangaren ilimi, Kiwon lafiya da sauran Bukatun Alummah.

A jawaban su daban daban Sabon shugaban gidauniyar reshen jihar Kaduna Muhammad Bello Gamo da kuma mai magana da yawun gidauniyar reshen jihar Kaduna Yusuf Ibrahim kudan, Sun bada tabbaci ga Muhammad Bashir lamido da mambobin Wannan Gidauniya a duk fadin Kasar nan cewa Zasu yi iya bakin kokari wajen tabbatar da nasarar wannan Gidauniya.

Kana kuma suka yi kira ga daukacin matasa da al’ummar jihar Kaduna da su bada goyon bayan nasarar Muhammad Bashir lamido da kuma kokarin sa na sake maido da Martaban Nigeria.

A cikin abubuwan da aka gudanar a wajen wannan taro sun hada harda Bada Takardan fara aiki ga wasu kalilan daga cikin Mambobin wannan Gidauniya domin fara aiki ka’in da Na’in.

Muhammad Bello Gamo matsayin Shugaban gidauniyar reshen jihar Kaduna, Sai Fauziyya Bello Matsayin Shugaban Mata, da Yusuf Ibrahim kudan a matsayin Sakataren Yada labarai da kuma wasu da dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *