Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel ( Fada da cikawa), ya kai ziyar girmama wa ga mai martaba sarkin Gaya, Alhaji Dr. Aliyu Ibrahim Gaya, tare da ganawa ta musamman da masu ruwa da tsaki na masarautar , kan wani riciki da ya faru mako guda da ya gabata a garin Kademi a karamar hukumar Gaya don warware matsalar.
Kakakin rundunar yan sandan jahar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne, ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aike wa da Idongari.ng, a ranar talata 23-1-2023.
Da yake gabatar da jawabinsa, kwamishinan yan sandan Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya bayyana cewa wannan rana ce, ta tarihi da ba zai taba mantawa da ita ba, domin suna samun nasara a aiyukan da suke gabatar wa, bisa addu’o’in da iyayen kasa da kuma Limamai ke yi akoda yaushe.
Ya kara da cewa addu’o’in da ake yi a masallatan masarautar Gaya suna zuwa kunnuwansu, wanda hakan yake karfafa musu gwiwa da cewar ba za suji kunya ba.
” Mai martaba sarki da mutanen wannan fada mai albarka, shaida ce akan cewar lokaci ya chanja muna cikin wani yanayi wanda idan ba a dawo ga Allah subahanahu wata’ala ba, an ci gaba da girmama shugaba musamman Sarki Uba ne wakili na Allah a doron kasa” CP Gumel”.
Kwamishinan yan sandan ya bayyana takaicinsa kan yadda girmama sarakunan yake neman gushewa.
CP Gumel, ya ce da wannan dalili ne ya kawo kukansa ga mai martaba sarkin Gaya domin ya wakilta jama’arsa dan a zauna da su , a lalubo bakin zaren warware matsalolin da suka faru a garin Kademi mako guda ya gabata.
” Sanin kowa ne dole ne mu tashi mu tsare jahar Kano baki daya, a yau idan kai waiwaye ka duba makotan mu babu wata jaha da ke da zaman lafiya sai jahar Kano, babu wata jaha da take da arzikin jama’a da dukiya kamar jahar Kano” Gumel.
Rahotan da jaridar Idongari.ng, ta tattara na cewar wani riciki ne ya faru tsakanin magoya bayan jam’iyar, NNPP da APC, a garin Kademi, a ranar 15 da 16 ga watan janairu 2024, bayan sanar da hukuncin kotun koli kan halastaccen gwamnan Kano.
Ricikin dai ya yi sanadiyar rauta bangarorin biyu, wanda yanzu haka wani ke kwance a gadon asibiti.Sabanin ya biyo bayan kunna wata waka da wani mai suna Habibu, wanda jami’an yan sandan Kanon, ke nema sakamakon guduwa da ya yi bayan faruwar wancan riciki da janyo raunta mutane da dama.
Kan wannan matsalar kwamishinan yan sandan ya tattauna da masu ruwa da tsaki na masarutar da tare kafa kwamitin da zai sulhunta bangarorin biyu nan mako guda.
A nasa jawabin mai martaba Sarkin Gaya, Alhaji Dr. Aliyu Ibrahim Gaya, ya godiya kwamishinan yan sandan da yan tawagarsa, bisa jajircewarsu na tabbatar da tsaro a koda yaushe.
Alhaji Dr. Aliyu Ibrahim Gaya, ya kara da cewa, abunda ya faru a Kademi bai ji dadinsa kuma za su dauki matakai don hakan bata sake faruwa ba.
Mai martaba sarkin , yaja kunnen masu unguwani, Dagatai da Hakimai duk wanda ya sake bari aka yi rigima ko tayar da tarzoma su kuka da kansu.
Ya kuma tabbatar wa da kwamishinan yan sandan cewar, daga yanzu duk wanda ake zargi da aikata wani laifi, su nemi masu unguwanni za su kawo musu wanda ake zargin a koda yaushe.
Bangarorin biyu sun amince da kwamitin sulhun na mutane 8, da zai tattauna da wakilan bangarorin biyu.
A karshe taron ya kare ne da yaba wa jami’an yan sandan bisa jajircewarsu, don tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin cikin a wanni 24.