Wasu da ake kyautata zaton yan bindiga ne, sun kai wa mahaifiyar gwamnan jahar Taraba hari, Jummai Kefas da kuma yar uwan gwamnan mai suna Atsi.
Lamarin ya faru ne akan hanyar Wukari zuwa Kente, a karamar hukumar Wukari.
Shugaban karamar hukumar Wukari, ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Weekend Trust , ta wayar tarho.
Rahotanni na cewa mutanen sun zo akan Babura, inda suka yi yunkurin tsayar da motar da mahaifiyar gwamnan ke ciki, amma daya daga cikin yan sandan dake yin rakiyar mahaifiyar gwamnan, ya yi harbin iska.
Ya kara da cewa harkawo yanzu , ba a tantance mutanen da suka zo akan baburan , masu garkuwa da mutane ne ko kuma yan bindiga inda ake ci gaba da gudanar da bincike.
Jaridar www.idongari.ng , ta ruwaito cewa shugaban karamar hukumar bai tabbatar da ko an kama daya daga cikin wadanda ake zargin ko kuma akasin haka ba.
Rahotanni na cewa yar uwar gwamnan, Atsi Kefas, ta samu raunin harbin bindiga, inda likitoci a Asibitin Koyarwa na Wukari suka duba lafiyarta gabanin garzaya wa da ita Abuja ci gaba da kula da lafiyarta.
Kakakin rundunar yan sandan jahar Taraba SP Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce abun ya shafi wata mota dake dauke da mutanen gidan gwanatin jahar , inda mace daya ta samu rauni.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto babban sakataren yada labaran gwamnan, Yusuf Sanda, don ji daga gareshi ya ci tura.