An kama ƴansintiri 10 kan zargin kashe limamin garin Mada

Spread the love

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce an kama aƙalla ƴansintiri 10 da ake zargi da mummunan kisan malamin addinin musulunci a jihar Zamfara.

A ranar Talata ne aka yi wa malamin Sheikh Abubakar Hassan kisan gilla inda kuma ake zargin ƴansintiri da hannu a lamarin da ya faru a ƙaramar hukumar Gusau.

Wata sanarwa da kakakin gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta bayyana cewa waɗanda ake zargi da hukumomi suka kama ƴansintiri ne ba askarawan jihar da aka ƙaddamar ba a baya-bayan nan.

Jajirtattun yan sandan Kano 14 sun samu karin girma daga SP zuwa CSP

Yan sandan Kano sun cafke Mutane 178 cikin watanni 2 bisa zargin aikata laifuka maban-banta

“Gwamnatin jihar Zamfara ta samu labarin mummunan kisan da aka yi wa Sheikh Abubakar Hassan Mada a garin Mada. Abun takaici ne da za a iya hana faruwarsa.

“Jami’an tsaro sun kama duk ƴansintirin da ake zargi da hannu a wannan ƙazamin lamari. Muna son yin ƙarin bayani cewa ƴan sintirin da ake zargi da hannu a kisan ba su da wata alaƙa da askarawan jihar Zamfara.” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Gwamnatin ta ce sakamakon binciken farko daga ƴansanda ya nuna cewa ɗaya daga cikin ƴansintirin da aka kama tsohon ɗalibin malamin da aka kashe ne. Bayanin zai taimaka wa hukumomi su fahimci lamarin tare da ɗaukan matakan da suka kamata.

A cewar gwamnatin, za ta gabatar da sakamakon binciken ƴansanda da zarar an kammala.

Ta kuma miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan malamin da kuma al’ummar garin Mada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *