An kama ɗaliban Najeriya kan zargin zamba ta intanet

Spread the love

Hukumomi a Najeriya sun kama mutum 50 da ake zargi da aikata almundahana ta intanet, akasarinsu ɗaliban jami’ar jihar Kwara.

Hukumar EFCC mai yaƙi da yi wa arzikin ƙasa zagon ƙasa cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis ta ce an kama ɗalibai 48 da wasu mutum biyu a maɓoyansu daban-daban sakamakon kwanakin da aka shafe ana sa ido.

EFCC ta ce ta gano wasu motocin ƙasaita tara sai kwamfutocin laptop 24 da kuma wayoyin hannu daban-daban a hannun mutanen da ake zargi, waɗanda aka ce suna rayuwa ta facaka.

Ba gudu ba ja da baya a sauye-sauyen da za mu kawo – Tinubu

An samu hatsaniya a majalisar dokokin jihar Zamfara bisa tabarbarewar tsaro

Hukumar ta kuma ce jami’anta sun bazama domin fitar da ƙasar daga ƙangin rashawa da sauran miyagun laifuka da ƴan yahoo ke yi.

Hukumar a shafinta na X ta wallafa hotunan kayayyakin da ta ƙwace daga hannun mutanen da ake zargi da tafka almundahanar da intanet.

A cewar EFCC, ba da daɗewa bane za a gurfanar da mutanen a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *