An Kama Barayin Shanu Da Mai Satar Mota A Jigawa

Spread the love

Rundunar yan sanda ta jihar Jigawa ta sake samun nasara a kokarinta na yaki da aikata laifuka, inda ta cafke mutane hudu da ake zargi da satar shanu da kuma mota a karamar hukumar Hadejia.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Shiisu Lawan Adam ya sanya wa hannu, rundunar ta bayyana cewa a ranar 18 ga watan Satumba, 2025, jami’an ’yan sanda da ke yankin Hadejia tare da hadin gwiwar kungiyar sa-kai ta Yanbulala sun kama wani mutum mai suna Isah Muhammad dan shekara 47 daga garin Mutum Daya a karamar hukumar Kirikasamma, dauke da shanu biyu da ake zargin an sato.

Sanarwar ta kuma ce a ranar 17 ga watan Satumba, 2025, jami’an ’yan sanda a Hadejia sun cafke wasu mutane uku da ake zargi da satar wata mota.

Wadanda aka kama sun hada da Amadu Dan Zaria dan shekara 45 daga karamar hukumar Malam Madori, da Salisu Ya’u dan shekara 25 da Musa Muhammad dan shekara 30, dukkansu daga Hadejia, inda aka sami nasarar kwato motar kuma bincike ya na ci gaba da gudana.

A karshe Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, CP Dahiru Muhammad, ya yaba wa jami’an bisa himma da kwazon su, tare da tabbatar wa al’umma cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da sintiri, domin kawar da masu aikata laifuka a fadin jihar.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba da sahihan bayanai da za su taimaka wajen dakile laifuka, tare da yin kira ga Al’umma da su kasance masu bin doka da kula da tsaro a kowane lokaci.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *