Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama dan sandan Bogi mai suna, Nasiru Shitu dan shekaru 33 mazaunin unguwar Kofar Waika, bisa zarginsa da bayar da hannu akan titi sanye da kayan yan sanda suna cutar jama’a.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana ga hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikewa da manema labarai a ranar litinin.
Sanarwar ta ce an kama wanda ake zargin ne bisa korafe-korafen da al’umma suka shigar ga rundunar saboda tare su da batagarin suke yi tare da cutarsu.
‘’ wannan ya biyo bayan samun korafe-korafe da mutane suka y ikan wasu batagari,suna sa Kaki na yan sanda suke tsayawa suna cutar da su’’
Ya kara da cewa bayan samun korafin kwamishinan yan sandan jihar CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayar da umarnin kara sanya ido a wuraren da suke aikata laifin.
Sai dai wanda ake zargi ya tabbatar da cewa yana yin shaye-shaye, kuma son aikin dan sandan ne yasa shi bayar da hannu sanye da kayan jami’an yan sanda.
Ya kara da cewa a baya an taba kamashi lokacin da yake bayar da hannun akan titi, kuma aka gargadeshi ya daina amma bai daina ba.
A cewarsa hatta iyayensa sunja masa kunne ya hakura ya daina sanya kayan tunda shi ba jami’in tsaron ba ne.
A karshe rundunar yan sandan ta ce zata gurfanar da matashin a gaban kotu da zargin yin sojan gona.