An Kama Dan Sandan Kwansitabulari Na Bogi A Kano.

Spread the love

Rundunar Yan Sandan jahar Kano, ta kama wani Dan Sandan Sarauniya na bogi, mai suna Salisu Bala , Dan Shekaru 31 mazaunin unguwar Kurna.

An kama Wanda Ake Zargin a ranar 14 ga watan Oktoba 2024, bayan Samun rahotanni daga unguwanni, Sabon Gari, Fagge da Koki dadai sauransu, kan cewar wadansu batagari suna fitowa a matsayin Yan Sandan Kwansitabulary suna cutar mutane.

Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa , ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aike wa da IDONGARI.ng , a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce bayan Samun rahotanne kwamishinan yan Sandan jahar Kano CP Salman Dogo Garba, ya ba da ga dukkan baturen Yan Sanda da suke Aiki a yankunan , suka Sanya Ido da fadada Sintiri duk inda aka ga irin wadannan batagari akamo su.

Yan Sandan Sarauniya ne suka kama wadanda ake Zargin sakamakon Bata mu su suna da yake Yi.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya kara da cewa an dawo dashi sashin binciken manyan laifuka dake shelkwatar Rundunar Yan Sandan Kano a unguwar Bompai.

Binciken Yan Sandan na farko-farko, ya gano Kakin Yan Sanda iri daban-daban a gidansa.

Rundunar ta ce Wanda aka kama din ba, Dan Sanda ba ne kuma ba Kwansitabulary ba ne, haka Kawai ya Yi gaban Kansa don cutar da jama’a.

Wanda Ake Zargin ya tabbatar wa da jami’an Yan Sanda cewar shi Dan Sandan Bogi ne.

A karshe Ruseendunar ta ce duk Wanda yasan matashin ya cuceshi ko ya zalince shi, ya shigar da korafinsa, don fadada bincike Kansa kafin a Gurfanar da shi a gaban kotun.

Muryar kakakin Rundunar Yan Sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa da kuma Wanda Ake Zargin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *