Jami’an bijilanti dake Unguwa Uku karamar hukumar Tarauni Kano, sun kama wani Danbori da Zargin Damfarar jama’a, ta hanyar Yi mu su karyar zai buga mu su kudin bogi na iskokai.
Adamu Abubakar Fiya-Fiya , shi ne kwamandan bijilanti na yankin Unguwa Uku , ya tabbatar wa da idongari.ng, cewar sun sami korafi ne Daga wani Matashi, Inda ya shaida mu su cewar Wanda Ake Zargin ya damfare shi kudi naira Dubu dari, don ya buga masa kudin bogi na iskokai.
Mutumin da ake Zargin Mai suna Mu’azu Kwanar Dangora, ya ce tabbas ya karbi kudin matashin da nufin zai buga masa kudin bogin , don a siyi Zuma, Turare da kuma Nono, Amma ya bukaci matashin ya kawo ganyen Tunfafiya guda 100.
Mu’azu Kwanar Dangora, ya kara da cewa bayan ya kawo masa ganyen Tunfafiyar, sai yaki hada masa , Amma matashin ya bukaci ya bashi kudinsa ne, sai ya dinga Yi masa barazanar cewar zai Tura masa Aljana , idan ya kara tambayarsa ko kuma zuwa wajensa.
Sai dai ya ce shi baya Tura Aljanun Amma ya Yi hakan ne domin ya tsorata shi.
Kwamandan bijilanti Adamu Abubakar Fiya-Fiya , ya ce wannan dalili ne ya Sanya su kamo Wanda Ake Zargin, kuma an samu kayan Tsafe-tsafe a wajen sa.
Akarshe ya ce za su mika Wanda Ake Zargin a Hannun jami’an Yan Sanda don fadada bincike akan sa.
- Zanga-zanga: An Saki Turawan Da Ake Zargi Da Hannu A Daga Tutar Rasha A Najeriya
- Mai kai wa ’yan ta’adda kakin sojoji ya shiga hannu a Kaduna