Jagoran haramtacciyar ƙungiyar IPOB ta kudu maso kudancin Najeriya, Simon Ekpa ya shiga hannu a ƙasar Finland bisa zarginsa da aikata laifukan ta’addanci.
Kafofin watsa labarai na ƙasar Finladn sun ruwaito cewa wata kotu a yankin Päijät-Häme ta tura Ekpa gidan yari bisa zarginsa da ingiza mutane su aikata laifuka.
Kotun ta ce Simon Ekpa tana yaɗa farfagandar a ware a kafofin sadarwa.
Bayan Ekpa kuma, kotun ta ce a kamo mata wasu mutum hudu bisa zarginsu da laifukan ta’addancin.
Ekpa, wanda ɗan Najeriya ne, wanda yake da izinin zama ɗan ƙasar Finland, an haife shi ne a shekarar 1985, kuma ya taɓa bayyana cewa yana jagorantar wata ƙungiya a Najeriya da take fafutikar kafa ƙasar Biyafara.
Ƴansanda sun ce suna zargin Ekpa da yaɗa manufofinsa ne daga ƙasar ta Finland da zummar haifar da tarzoma, wadda ke cutar da fararen hula da sauran laifuka a yankin kudu maso kudancin Najeriya.
A wani faifan bidiyo da ya a game da zaɓen 2023, ya ce ba za a yi zaɓe ba a yankin kudu maso kudu.