’Yan sanda sun kama wani korarren jami’in shige da fice a yayin da yake kokarin sayar da makamai ga ’yan ta’adda.
Kwamishinan ’Yan Sanda na Babban Birnin Tarayya, Olatunji Rilwan Disu, ya bayyana cewa an kama jami’in ne a hanyarsa ta kai wa ’yan ta’addan bindigogi a yankin Zuma da ke Ƙaramar Hukumar Bwari.
Da yake jawabi a hedikwatar rundunar, CP Olatunji Rilwan, ya bayyana cewa dubun korarren jami’in tsaron ta cika ne a ranar 27 ga watan Fabrairu, 2025.
Disu wanda ke bayani kan ayyukan rundunar daga watan Janairu zuwa Maris na 2025, ya ce an ƙwato wasu sabbin manyan bindigogi biyu ƙirar CZ Scorpion EVO 3 A1 a hannun wanda ake zargin.
Ya bayyana cewa rundunar tana tsare da wanda ake zargin yana amsa tambayoyi.
- Yan Sanda Sun Tabbatar Da Tsintar Gawar Tsohon Shugaban Hukumar Shige Da Fice A Hotel
- Yan Sandan Kano Sun Bankado Gungun Mutanen Da Suke Yaudarar Samari A Facebook Ciki Harda Yan Sandan Bogi.
Ya kara da cewa rundunar yaƙi da masu garkuwa da mutanen ta kuma halaka wasu ’yan bindiga bakwai a wani samamen da ta kai maɓoyar ɓata-garin a ƙauyen Gidan-Dogo da Daji Kweri da ke kan iyakar Abuja da Jihar Neja.
Ya ce an kama ’yan bindiga ɗauke da bindigogi ƙirar AK47da sauran wasu makamai a yankunan.
A cewarsa, jimillar ’yan fashi da makami 59 da masu garkuwa da mutane tara da masu kai musu bayanai 10 ne dubu su ta cika a tsawon lokacin