Rundunar yan sandan jihar Jigawa, ta samu nasarar kama wasu mutane da ake zargi lalata Taransifoma, a karamar hukumar Hadejia.
Kakakin rundunar yan sandan jihar SP Shisu Lawan Adamu, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwar ta ce an kama batagarin lokacin da suke barnata na’urar wutar lantakin, wadanda suka fito daga jahohin Kano, Bauchi da kuma Jigawa.
Haka zalika ana zargin sun kware wajen lalata taransifoma tare da siyar da ita a garuruwa dabanm-daban.
Wadanda ake zargin sun hada sun hada Haruna Musa dan shekaru 36 , Hussaini Innocent, Abubakar Yakubu , Zakariyya Mohammed, Mamman Danladi , Khalifa Yahaya, Ibrahim Mohammed, Ali Ibrahim.
- Yan Sanda Sun Kama Masu Yin Sojan Gona Da Sunan Su A Kano
- Matasa sun kashe ’yan bindiga 6 sun sha alwashin kare kansu
Hakazalika, an kara kama wasu matasan a garin Bamaina a lokacin da suke kona wayar wutan lartarki a wata makaranta wadda kudin wayar yakai naira miliyan bakwai (7).
SP Shisu Adamu, ya kara da cewa tuni sun gurfanar da wasu daga cikin matasan, a gaban kotu, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike don kamo sauran da suka gudu da kuma masu siyan kayan satar.