An cafke wata mata da ta sayar da kananan yara 42 domin aikin bauta a shekaru biyar da suka gabata.
Matar mai shekaru 45, wadda ke gudanar da mummunar sana’ar a Jihar Kwara ta sanar da haka ne a caji ofis bayan ’yan sanda sun damke ta a yankin Ijora Badia da ke Jihar Lagos.
Ta shaida wa hukuma cewa, “Na sayar da kananan yara sama da 42 ga mutane daban-daban, wadanda yawancinsu a Legas suke.
Rundunar yan sandan Nijeriya ta cafke wanda ya kashe Nabeeha,
“Na fi sayar da kananan yara ’yan shekaru 7 zuwa 12 kuma Lagas nake kawo su inda suka aikin bauta.”
Rundunar ’yan sandan jihar Legas ta ce jami’anta sun kubutar da kananan yara uku, namiji da mata biyu, daga hannun matar.
Kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin, ya ce wadda aka kaman ce jagorar wani gungun masu sayar da kananan yara kuma an kama ta ne bayan shafe watanni ana bincike da kuma farautar ta.
CP M.U. Gumel, ya karbi nambobin yabo daga NDLEA da sauran kungiyoyi a Kano
Hundeyin ya ce kafin a kama ta, rundunar ’yan sandan jihar Kwara na neman ta ruwa a jallo kan zargin hannunta a bacewar kanana yara.
A cewarsa, an kama ta ne a lokacin da ta kawo wasu kananan yara 52 aikin bauta Legas ba tare da izinin mahaifansu ba.
Kano: Hukumar KAROTA ta musanta wani rubutu da ta gani yana yawo da sunan ta
Jami’in ya ce hukumomin ’yan sandan jihar Kwara sun gano 11 daga cikin yaran da ake nema, a lokacin bincike kuma matar bayyana inda ta kai wasu daga cikinsu, kuma kokarin gano inda ragowar suke.