Rundunar yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar baturen yan sandan karamar hukumar Rano, tare da kama matasa 27 da ake zargi da yin sanadiyar mutuwarsa da kuma lalata motocin yan sanda 10.
Rundunar yan sandan jihar Kano, ta bayyana samun wani labarin a matsayin mara dadin ji da ya faru, a ranar 25 ga watan mayu 2025 da misalin karfe 8:15PM.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, da yau litinin.
A cewar sanarwar, rikicin ya samo asali ne bayan jami’an yan sandan sun kama wani matukin babur mai suna Abdullahi Musa, sakamakon korafe-korafen da al’umma suka yi akan yadda yake yin tukin ganganci da kuma zarginsa da shan kayan maye.
Bayan haka ne matashin ya fara nuna alamun rashin kuzari lokacin da yake tsare, inda aka garzaya da shi babban sibitin Rano, inda ya rasu da safiyar Litinin yayin da ake kula da lafiyarsa.
Rasuwar matashin ta tayar da hankula, inda wasu bata-garin matasa suka farwa Ofishin yan sandan Rano, sannan suka lalata wasu sassansa,tare da farfasa motoci 10 da kone wasu guda 2 da yin sata tare da jikkata baturen yan sandan .
- Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Da Bulala 150 Ga Wanda Aka Samu Da Laifin Kunnawa Mutane Wuta A Masallaci
- Yan Sanda Sun Gaiyaci Harrison Gwamnishu Kan Wallafa Batan Mutane A Anambra.
Bayan haka ne aka garzaya dashi asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa lokacin da ake duba lafiyarsa.
Yanzu haka dai ta ce ta kama mutane 27 dake alaka da wannan aika-aika kuma tuni al’amura suka dawo daidai a yankin.
Kwamishinan Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Bakori, ya kai ziyara garin Rano, inda ya duba irin barnar da aka yi, tare da yin ta’aziyya ga mai martaba Sarkin Rano, Ambasada Dakta Mohammed Isah Umar (Autan Bawo 19).
Haka kuma, Kwamishinan ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike na gaskiya don yin adalci domin gano musabbabin tashin hankalin.
Akarshe rundunar ta jajantawa yan uwa da iyalan baturen yan sandan da ya rasa ransa a bakin aiki , tare da kira ga al’ummar jihar su daina daukar doka a hannu.