Kwamitin tsaro na yankin Unguwar Danbare, a Karamar hukumar Kumbotso Kano, sun samu nasarar cafke wasu Matasa hudu, bisa zarginsu da yin kwace da kuma kwashe kayan Amare.
Jaridar idongari.ng, ta ruwaito cewa, dubun matasan ta cika ne bayan da al’ummar unguwannin, Danbare, Yawan Dawaki da kuma Dorayi Babba, Suka koka kan sabon salon da matasan suke Yi na yaudara da wasu Mata wadanda suke yin sallama a sabbin gidaje, Ana budewa sai mazan su fada gidan su kwashe kayan amare.
- Yau Ake Daura Auren Sadiya Haruna A Karo Na 9
- Lauyoyin Aminu Ado Bayero sun fice daga shari’ar dambarwar masarautu
Haka zalika Ana zargin matasan sun kware wajen balle gidajen mutane bayan sun tafi unguwa, inda suke Yi mu su satar kayayyaki da sauran muhimman abubuwa.
Wannan dalilin ta sanya yan kwamitin unguwannin, Kara sanya ido ga wadanda suke shige da fice a yankin har Suka samu nasarar Kama matasan hudu da ake zargi da hannunsu wajen aikata sata da balle gidajen jama’a.
Shugaban kwamitin tsaron Unguwar Danbare, Alhaji Baba Habu Mika’ilu, ya bayyana wa jaridar idongari.ng, cewa sun Kama matasan ne, a lokacin da Suka dawo daukar Baburunsu.
Tunda farko an biyo su ne amma suka gudu, Kafin a Kama su.
A karshe Baba Habu, ya ce za su mika su hannun Jami’an yan sanda, don fadada bincike akansu.