Rundunar yan sandan jihar Kano ta kai sumame tare samun nasarar kama mutane 33, wadanda ake zargi aikata laifukan daba a sassan jihar, daga ranar 23 ga watan Afrilu zuwa 28 ga watan afrilun 2025.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Litinin.
Sanarwar ta ce an kai sumamen ne karkashin jagorancin Oc Anti daba, CSP Bashir Musa Gwadabe, bayan samun sahihan bayan sirri kan wadanda ake zargi sun addabi al’umma da fadace-fadacen daba da kuma ta’ammali da miyagun kwayoyi a birnin Kano.
- Rundunar Yan Sandan Kano Ta Mika Kwayar Tramadol Ta N150m Ga NDLEA
- Tsohon Sakataren NUJ Na Kasa Ya Mutu Yana Da Shekaru 91
SP Kiyawa ya kara da cewa an kama mutane dauke da muggan makamai, kwayoyi da kuma kayan da ake zargin sun yi wa jama’a fashin su.
Ya ce za a gurfanar da mutanen da zargin a gaban kotu da kayayyakin da aka samu a wajen su da zarar an kammala gudanar da bincike.
Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori , ya yabawa al’ummar jihar, bisa hadin kai da goyon bayan da suke basu akoda yaushe, inda ya yi kira agare su da su ci gaba da basu bayanan sirri don kakkabe aiyukan batagari.