An Kama Mutum 5 Kan Satar IPhone 13 Yayin Sallar Tahajjud A Abuja

Spread the love

Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, Abuja sun cafke wasu mutum biyar da ake zargi da satar iPhone 13 a yayin sallar Tahajjud a Masallacin Al-Nur da ke Wuse II a Abuja.

Kwamishinan ’yan sandan Abuja, CP Benneth Igweh ne, ya bayyana haka yayin da yake gabatar da wadanda ake zargin a ranar Litinin.

Ya ce, an kama waɗanda ake zargin ne bayan mai wayar da ke rukunin gidaje na Hampton, a yankin Maitama  Abuja, ya kai rahoto a ofishin ‘yan sandan Wuse da safiyar Lahadi.

Ya ce an sace masa wayarsa kirar iPhone 13 a masallacin a yayin sallar Tahajjud.

Bayan kai rahoton, ‘yan sanda suka bazama, don nemo wayar .

A cewarsa ɓarayin wayar sun kai ta  rukunin gidaje na Djomes Suites mai lamba 28 Agadez a Wuse II Abuja.

Ya kara da cewa, nan da nan jami’an ‘yan sandan suka zagaye rukunin don gano inda wayar ta ke.

A nan ne aka kama wadanda ake zargi da sace wayar.

“Binciken ’yan sanda ya gano yadda waɗanda ake zargi suka saci manyan wayoyi 23.”

Kwamishinan, ya ce an samu mota kirar Mercedes Benz C300 wanda ba a yi wa rajista ba.

“Ragowar kayan da aka kwato sun haɗa da talabijin da kuma injin dumame, (microwave) daga hannun wadanda ake zargin.

“Ragowar kayan da aka kwato sun haɗa da talabijin da kuma injin dumame, (microwave) daga hannun wadanda ake zargin.

“Za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *