An kama mutum biyu da ake zargi da bai wa masu garkuwa kariya a Jigawa

Spread the love

Rundunar ƴan sanda a jihar Jigawa ta ce jami’anta sun kama wani mutum mai shekara 40 da wani mai shekara 30 dukkansu a ƙaramar hukumar Gumel ta jihar bisa zarginsu da bai wa wani da ta kira riƙaƙƙen ɗan fashi da makami kuma mai garkuwa da mutane kariya.

Ɗan fashin dai ya kasance kan gaba a jerin mutanen da rundunar take nema ruwa a jallo.

Rundunar ta bayyana haka ne cikin bayanin da ta wallafa a shafinta na Facebook inda ta ce ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ya bayyana cewa shi ne yake tuka ɗan fashin a kan babur idan ya je ƙauyen yayin da ɗayan kuma ya ce mutumin da ake nema ruwa a jallo yana kai masa hulunansa domin ya wanke su kasancewar ita ce sana’arsa.

ASP Abubakar Isah, Kakakin rundunar ƴan sandan a Jigawa ya ce an ƙara ƙaimi domin kama mutumin da ake zargi ɗan fashi ne.

Ya kuma ce yayin samamen da ƴan sanda suka kai lunguna da saƙo, an kama mutum 25 da ake zargi da kasuwancin miyagun ƙwayoyi.

Kakakin rundunar ya ce da zarar an kammala bincike a sashen binciken manyan laifuka da ke Dutse, za a gurfanar da mutanen da aka kama a kotu domin su fuskanci tuhuma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *