Rundunar Yan Sandan jahar Kano ta samu nasarar kama Wani mutum, Mai suna Aminu Abdullahi, Dan Shekaru 50 dake zaune a unguwar Kofar Nasarawa, bisa Zargin sa da yin Sojan gona ta hanyar Bata suna, Damfara da kuma sata.
Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aike wa manema labarai, a ranar Talata.
SP Abdullahi Kiyawa, ya ce tun a ranar 22 ga watan Nuwamban 2024, suka karbi korafi daga wajen Wani Mai suna Sunusi Aminu, a ofishin Yan Sanda na Gwale, da cewar ” Wani mutum Mai suna Aminu, yaje shagonsa tare da gabatar da Kansa matsayin kanin Sheik Dr. Abdullah Usman Gadon Kaya, har ya siyi katon biyu Taliya, kan kudi naira Dubu Talatin da biyar”.
- Zargin Kone Masallata: A Shirye Na Ke Duk Irin Hukuncin Da Za A Yi Mun: Shafi’u Abubakar
- Bankin GT Ya Roki Kotu Ta Cire shi A Karar Da Aka Shigar Da Wasu Bankuna Don Hana Su Rike Kudaden Kananan Hukumomin Kano
Bayan ya Yi siyayyar ne sai ya nuna mu su cewar ya Yi mu su Taransifa, Amma kudin ba su ga Alert ba, sai dai sakamakon alakanta Kansa da Sheik Dr. Abdullah Gadon Kaya, ne suka amince da shi , cewar za su ga Alert din daga baya.
” Bayan ya tafi shi wannan Mai shago , ya duba asusun bankinsa sai ya ga kudi Bai shigo ba, Inda ya fara Zargi har ya shigar da korafi a wajen Yan Sanda “.
Sanarwar ta kara da cewa bayan karbar korafin ne kwamishinan yan Sandan Kano CP Salman Dogo Garba, ya bayar da umarni ga Baturen Yan Sandan Gwale SP Abdulrahim Adamu, kan cewar duk Inda mutumin yake a tabbatar da an kamo shi, kuma aka samu nasarar cafke shi.
Idongari.ng, ta ruwaito cewa Wanda Ake Zargin ya zuwa shagunan mutane ya Yi siyayya amma ya cuce su.
SP Abdullahi Haruna, ya ce zuwa yanzu an samu mutane 22 da suke korafi kan mutumin, cikinsu harda Sheik Dr. Abdullah Usman Gadon Kaya.
Rundunar ta ce duk Wanda yasan mutumin ya cuce shi , to Yana da damar shigar da korafinsa.
Wanda Ake Zargin ya amsa laifinsa tare da bayyana nadamarsa ga mutanen da ya cuta.
A karshe Rundunar ta ce da zarar ta kammala gudanar da bincike, za a Gurfanar da shi a gaban kotu.