An kama wani matashi kan zargin kisan mahaifinsa a Kano

Spread the love

Hukumar tsaro ta Civil Defence a Kano ta ce kama wani matashi mai suna Alkasim Ya’u bisa zargin kashe mahaifinsa.

Lamarin ya rafu ne a ranar Juma’a da dare a unguwar Tudun Yola da ke karamar hukumar Gwale.

Mai magana da yawun hukumar Ibrahim Abdullahi ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, inda ya ce mahaifin yaron mai suna Ya’u Mohammed wanda ɗan asalin jihar Katsina, ya kawo ɗan nasa ne Alkasim asibitin Dawanau don duba lafiyarsa saboda matsalar kwakwalwa da yake da shi.

Ya ce bayan zuwansu asibitin aka ce musu ba za su iya ganin likita ba sai washegari ranar Asabar, 6 ga watan Janairu.

“Maimakon su koma Katsina, sai mamacin ya yanke shawarar kwana a gidan ɗan uwansa da ke unguwar Tudun Yola.

“Alkasim ya faki idon mahaifinsa lokacin da yake cin abinci sai ya buga masa tangaram (plate) ɗin da yake cin abinci da shi. Babu kowa a gida lokacin saboda mutane sun tafi sallar Juma’a,” in ji Abdullahi.

Ya ce daga bisani bayan dawowar mutane sai aka samu labarin abin da ya faru, inda aka garzaya da mahaifin asibiti inda kuma rai ya yi halinsa a jiya Asabar.

Jami’in hulɗa na rundunar ta Cibil Defence ya ce tuni aka miƙa matashin hannun ƴan sanda domin ci gaba da bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *