Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta samu nasarar kama wasu mutane da ake zargi da laifin garkuwa da mutane
Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
SP Kiyawa, ya ce ana zargin mutanen da laifin yin garkuwa da wata mata mazauniyar karamar hukumar Minjibir inda suka kai ta jihar Jigawa don neman kudin fansa.
Bayan samun labarin ne aka tura dakarun yan sanda, inda suka yi arangama da wadanda ake zargin har suka harbe wasu daga cikinsu sannan suka kama sauran .
Haka zalika an kwato makamai, a hannunsu kuma an kubutar da matar ba tare da an biya kudin fansa ba.
- Digiri Dan Kwatano : Majallisa Ta Amince A Ba Wa Dan Jaridar Da Ya Bankado Digirin Bogi Tsaro.
- Ya Mutu Yana Kokarin Satar Wayar Lantarki A Kano