An Kama Yan Sadan Bogi 5 Da Zargin Cutar Da Mutane A Kano.

Spread the love

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta kama wasu gungun mutane 5 da ake zargi da aikata laifin yin sojan gona a matsayin jami’an yan sanda.

Yan sandan bogin an kama su lokacin da suke yawo a wurare dabam-daban don cutar al’umma ta hanyar yi musu kwacen kudi.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce dakarun su da suke kai daukin gaggawa na musamman ne suka yi nasarar kama wadanda ake zargin bayan samun sashihan bayanan sirri.

Wadanda ake zargin sun hada da , Aliyu Abbas mai shekaru 35 da Sani Iliyasu mai shekaru 47 da Ashiru Sule mai shekaru 41 da Abubakar Yahaya mai shekaru 45 da kuma Adamu Kalilu mai shekaru 45.

SP Abdullahi Kiyawa, ya kara da cewa  an samu ID Card na yan sand ana bogi da Ankwa da kudin CFA 2,500 da kudin Nijeriya a yagaggu da kuma motar da suke yawo a cikin ta.

Binciken yan sanda na farko-farko ya tabbatar da cewa wadanda ake zargin sun tabbatar da cewa, sun dauki lokaci suna yawo a wurare dabam-daban don cutar jama’a, a jahohin Kaduna, Katsina da kuma Kano.

Rundunar yan sandan ta yi kira dukkan wadanda suke da kokari kan irin mutanen da suke karbe musu kudi da sunan jami’an yan sanda, su garzayo shelkwatar rundunar don ganin wadanda ake zargin ko za su gane su.

Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya godewa al’ummar jihar kan hadin kan da suke bayarwa a koda yaushe, tare da yin kira a gare su , a duk lokacin da suka ga wani abu da basu amince dashi bas u yi gaggawar sanarwa a ofishin yan sanda mafi kusa.

A karshe rundunar ta ce zata gurfanar da su a gaban kotu don su fuskanci hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *