An kama yaran mista Ibu kan zargin satar gudunmawar miliyan 55 na jinyarsa

Spread the love

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama ɗa da kuma ɗiyar fitaccen jarumin fina-finan barkwancin nan na Najeriya, John Okafor, wanda aka fi sani da Mista Ibu, bisa zargin satar gudunmawar kuɗin da aka shirya domin jinyar jarumin.

Ana zargin Onyeabuchi Okafo da Jasmine Okekeagwu da laifin “daukar wayar jarumin tare da yin kutse cikin bayanan bankinsa”, kafin suka sace naira miliyan 55.

Kuɗaɗen dai na daga cikin gudunmawar kuɗaɗen da masoyan jarumin suka bayar domin jinyarsa, bayan ya yi fama da doguwar rashin lafiya a bara.

Cutar ta yi sanadin yanke kafar Okafor daya. An kuma yi wa tauraron nollywood din tiyata biyar, in ji iyalansa.

Hukumomin ƙasar dai sun ƙwato naira miliyan 50, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na ƙasar suka ruwaito kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, ASP Mayegun Aminat ya bayyana.

Ƴaran nasa da ake zargin na shirin tserewa ne zuwa Birtaniya, a cewar Aminat.

Kafafen yaɗa labarai na ƙasar sun kuma ruwaito cewa wata kotu a Legas ta saki mutanen biyu kan belin Naira miliyan 15 yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.

Ana sa ran za su gurfana a gaban kotu a watan Maris don ci gaba da sauraren karar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *