Akalla wakilan kasashen Duniya 56, ne za su halarci babban birnin Accra dake ƙasar Ghana, don gudanar da taron tattaunawa kan hanyoyin da za a inganta harkokin sadarwar Internet.
Taron karo na biyu wanda kuma shi ne na karshe zai gudana a, Ghana a ranakun 23 zuwa 25 ga wannan watan Afrilu 2024 , bayan da aka kammala zagayen farkon a birnin Abuja a Najeriya.
A yayin taron na Abuja, Paradigm Initiative ta gayyaci ma su fada aji daga ɓangaren Gwamnatin Tarayya da bangarorin ma su zaman kansu, da kuma kungiyoyin da bana Gwamnati ba.
An tattauna tare da tafka muhawara kan hakkokin bil’adama a kafar Internet, musamman a Najeriya da kuma duba yadda hakkin yake bukatar samun wajen dogara daga mahukunta, hakan ne ya sanya aka tattauna kan bukatar samar da kudirin dokar da zata kula da kare hakkin al’umma a Internet.
Khadija El -usman Ita ce Shugabar Shirye Shiryen Kungiyar a Nigeria ta bayyana cewa Taron zai taimaka wajen Kare Hakkin ko wanne Dan Adam matukar yana Amfani da kafar internet.
Haka zalika An ba wa shugabanni shawarar inganta Kafafen internet.
- An Haramta Dukkan Fina-finan Dake Nuna Daba Da Daudu A Kano
- Tinubu ya sa hannu kan dokar bai wa ɗalibai bashin karatu
Barista Yusif Abdullahi Abdulkadir guda Daga Cikin Ma’aikatar sharia ta Gwamnatin Tarayyar Nigeria, ya Bayyana cewa Akwai dokar da ta bayar da dama wajen Ganin Kare Hakkin Gwamnati Dama Na Masu Amfani da Kafafen sadarwa wannan, yasa ya sake jaddawa kowanne Bangaren ya kasance ya kiyaye Doka.
Wata Yar Jarida Nusaiba Abdulaziz Muhammad , da ta wakilci Jihar kano, ta mika shawarar tabbatar da anyi yaki da Ma su rubutun Labaran Karya a kafafen sadarwa, ka zalika ta bayyana Yadda Gwamanatin kano ke kokari wajen Inganta Amfani da Kafar internet din ta Hanyar shigo da sabbin tsare tsaren Zamani a Mulkin Gwaman Abba kabir Yusif Wanda ya kasance Abin a yabawa Gwamnatin ta kano.
Wannan dai shi ne Karo na Goma 11 da Kungiyar Paradigm Initiative tare da Hadin Gwiwar Kingdom of Netherlands da ma jami’ar UNIMAC UNIVERSITY Of MEDIA ART & COMMUNICATION da african digital rights network ke Daukar Nauyin Shirya irin wannan taro ga Kasashen Nigeria da Ghana.
Ko a shekarar da ta gabata Wakilan Kasashen Africa 54 ne suka Halarci Taron karo na 10 a Nairobi Babban birnin kasar Kenya.