Rundunar ‘yansandan jihar Taraba ta karrama wasu jami’anta huɗu, saboda ƙin karɓar cin hancin naira miliyan 8.5 dagha wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne a lokacin da suke aiki a wani shingen binciken ababe hawa.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, David Illoyalonomo ne ya karrama jami’an huɗu a shalkwatar rundunar ‘yansandan jihar.
Mista Illoyalonomo ya ce jami’an sun nuna halin dattako, da ɗaga darajar aikin ɗansanda a idonduniya.
Kwamishinan ‘yansanda ya ce zai gabatar da jami’an huɗu ga babban sifeton ‘yansanda na ƙasar, Kayode Egbetokun, domin yi musu ƙarin girma da kuma duba yiyuwar karrama su da lambar yabo.