An kashe dukkanin ƴan bindiga da ke addabar jihar Kebbi

Spread the love

Gwamnatin Jihar Kebbi ta ce jami’an tsaro sun samu nasarar kashe dukkanin manyan ƴan bindiga da ke kai hari a wasu sassan jihar.

Inda ta ce hakan ya sa a yanzu manoma sun samu damar fita gonaki domin yin noma fiye da lokutan baya.

Kwamishinan watsa labarai na jihar Alhaji Yakubu Ahmed Birnin kebbi ne ya bayyana hakan a cikin wata hira da BBC.

Sai dai a cikin hirar kwamishinan watsa labaran ya fara ne da bayyana irin nasarorin da ya ce gwamnan jihar ya samu a cikin shekara ɗaya kan Mulki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *