Wani rahoto ya bayyana cewa mutane ashirin ne suka rasa rayukansu sakamakon tarzoma da ta ɓarke a yayin gudanar da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya.
Rahoton wanda kamfanin Beacon Consulting, mai nazari kan tsaro ya fitar ya yi nuni da cewa an kashe mutanen ne a jihohi shida da ke faɗin ƙasar.
A cewar rahoton an samu ɓarkewar tarzoma ne a jihohi 10 da suka haɗa da Adamawa da Borno da Gombe, da Jigawa da Kaduna da Kano da Kebbi da Nasarawa da Neja da kuma Yobe.
Kamfanin ya ce jihohin da aka samu rashin rayuka sun haɗa da Neja inda aka kashe mutum shida, sai jihar Borno inda aka kashe mutum huɗu, da Kaduna inda mutum uku suka rasu.
An samu rahoton mutuwar mutane huɗu a Jihar Kano, inda aka kashe mutum ɗaya a Kebbi, sannan mutane biyu ne suka mutu a Jihar Jigawa.
Rahoton ya ƙarƙare da cewa jami’an tsaro sun gaza a yunƙurinsu na tabbatar da cewa zanga-zangar ta gudana ba tare da tashin hankali ba.
“Ranar farko ta zanga-zangar ta nuna cewa jami’an tsaro da jami’an gwamnati sun yi ƙoƙarin hana zanga-zangar ko kuma tabbatar da an yi ta cikin lumana amma hakan bai yi nasara ba sakamakon yawan Jama’a da suka fito zanga-zangar a jihohi da dama.”
Har yanzu dai hukumomi ba su fitar da alƙaluma a hukumance ba kan lamarin.