An kashe Sarauniyar Kirifto

Spread the love

An kashe wata mata ƴar Bulgeriya da ta tsere wa hukumomi shekara bakwai da ta gabata.

Ruja Ignatova – wadda aka fi sani da CryptoQueen – tana cikin ‘Jerin mutanen da hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, FBI ke nema ruwa a jallo bayan an zarge ta da yaudarar miliyoyin mutane su saka hannun jari a harkar kuɗin kirifto na bogi mai suna OneCoin.

Ta bace a shekarar 2017 bayan an zarge ta da yin sama da fadi da dala biliyan hudu na masu saka hannun jari.

Wasu majiyoyi sun shaida wa BBC cewa wani ƙasurgumin mai aikata laifuka a Bulgeriya ya bai wa hukumar CIA bayanai kan kisan gillar da aka yi mata kafin shi ma aka kashe shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *