Rundunar sojin Najeriya ta sanar da korar wasu jami’anta biyu waɗanda aka samu da laifin satar wayoyin wutar lantarki a matatar Dangote da ke jihar Legas.
Tun da farko dai, a baya-bayan nan ne wasu jami’ai na kamfanin tsaro mai zaman kansa da kuma wasu sojoji suka kama waɗanda ake zargin, Kofur Innocent Joseph da Lance Kofur Jacob Gani bisa laifin sata.
Wata sanarwa da darektan yaɗa labarai na rundunar sojin Najeriya, Manjo-janar Onyema Nwachukwu, ya fitar ranar Litinin, ya ce an samu mutanen biyu da laifin barin wurin aikinsu yayin binciken da aka gudanar.
Nwachukwu ya bayyana cewa waɗanda ake zargin sun gaza yin aikinsu yadda ya kamata da kuma saɓa wa dokokin aikin soja kamar yadda yake a sashe na 57.
- Ƙaruwar fursunoni ma su dakon shari’a na janyo cunkoso a gidajen yarin Kano
- Sojojin Najeriya sun gano gidan gasa burodi na mayaƙan ISWAP a Borno
Ya ce bayan kammala bincike ne, rundunar ta ɗauki matakin sallamar jami’an biyu tare da miƙa su ga hukumomin da suka dace domin gurfanar da su gaban kotu, domin hakan ya zama izina ga sauran jami’an tsaro da ke shirin aikata irin wannan laifin.
“Muna da zimmar ganin mun ci gaba da jajircewa a kan aikinmu na kare ƴan ƙasa. Muna kira ga al’umma da su ci gaba da ba mu goyon baya a ƙoƙarin mu na samar da tsaro da kuma ɗabbaka zaman lafiya a faɗin ƙasa,” in ji sanarwar.