An kubutar da matar basaraken gargajiyar da aka kashe, marigayi Oba Olusegun Aremu-Cole wanda aka kashe a fadarsa ranar Alhamis.
An dai yi garkuwa da mai dakin nasa a ranar Alhamis da daddare tare da wata mata guda. wanda ba a tantnace ko wace ce ba, a ƙaramar hukumar Ekiti ta jihar Kwara.
An kuɓutar da su ne a daren ranar Litinin kuma sun isa garin Koro da misalin karfe 10:45 na dare.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, Ejire-Adeyemi Toun, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
Ko da yake bai bayyana sunan mutum na biyu da aka kubutar ba, rahotanni sun ce ’yar sarauniyar ce.
Kisan Nafi’u: Shari’ar Hafsat Chuchu Ta Samu Tsaiko.
Yan Najeriya su guji murnar wuce iyaka idan Eagles suka doke Bafana Bafana’
A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan, aikin ceton ya biyo bayan wani aikin hadin gwiwa da jami’an hukumar tsaron farin kaya (DSS) da ‘yan sanda da sojoji da ‘yan banga da mafarauta suka yi.
Ya ce jami’an tsaro sun kutsa cikin dajin da ke tsakanin jihohin Kwara da Ekiti bayan da Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, ya bayar da umarnin tura wani jirgin sama na ‘yan sanda domin binciken cikin dajin.
“Wannan aiki ceton ya kai ga nasarar ceto matar marigayin da kuma wani mutum daya a ranar 5 ga watan Fabrairun 2024.”
Sanarwar ta kara da cewa tuni aka haɗa waɗanda aka kuɓutar din da iyalansu, cikin jin dadi.
“A ci gaba da binciken, Sufeto Janar na ‘yan sanda IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya amince da tura jami’an ‘yan sanda ta jirgin sama domin bincike ta sararin samaniya domin taimaka wa Kwara da jihar EkitiI.”
Ejire-Adeyemi ya kara da cewa, “aikin ceton ya kuma kai ga kama wasu maza 13 da ake zargi da hannu a yanzu haka.”
“Wadanda aka kama dai suna fuskantar tambayoyi masu karfi da nufin taimakawa wajen cafke ‘sauran mutanen da ke da alhakin kai harin baki daya.”