An kuɓutar da ‘ya’yan ɗan majalisar Zamfara bayan wata 17 da sace su

Spread the love

Ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro tare da hadin gwiwar ƴan sanda sun ceto ‘ya’ya mata biyu na wani ɗan majalisar jihar Zamfara da aka yi garkuwa da su wata 17 da suka gabata.

Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa a ranar Talata ne aka miƙa yaran biyu, Maryam da Nana Asma’u ga mahaifin nasu Aminu Ardo a hedikwatar ƴan sanda ta ƙasa da ke birnin Abuja.

A lokacin miƙa wa ɗan majalisar ‘ya’yan nasa, mataimakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Isuku Victor ya ce mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro Mallam Nuhu Ribaɗo ne ya jagoranci ƙoƙarin ceto yaran tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro.

A watan Nuwanbar 2022 ne ƴan bindiga suka kai hari gidan Aminu Ardo a Jangebe da ke jihar Zamfara tare da yin garkuwa da matarsa da kuma ƙananan yaransa huɗu.

Mahaifiyar yaran da kuma biyu daga cikin yaran sun samu kuɓuta bayan da rahotonni sujka ce sun gudu daga inda [‘yan bindigar suka tsare su, inda suka bar sauran biyun Maryam da Nana Asma’u a hannun masu garkuwar.

CSP Victor ya ce yaran sun fuskanci wahalar rayuwa a lokacin da suke tsare a hannun ‘yan bindigar ciki har da shan ruwan rafuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *