An Kubutar Da Budurwar Da Aka yi Garkuwa Da Ita A Kano A Dajin Gubuchin Jahar Kaduna.

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Kano, ta cafke wasu mutane biyu da ake zarginsu da yin garkuwa da wata budurwa mai suna Hafsat Nuhu, mai shekaru 20, yar asalin kauyen Zarewa a karamar hukumar Rogo a jahar.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aike wa da manema labarai a ranar Litinin.

Sanarwar ta ce sun samu korafi a ranar 18 ga watan Yuli 2024, daga wajen mahaifin budurwar, cewar wasu mutane sun shigo gidansa cikin dare sannan suka dinga dunkansa, har suka bukaci ya biya kudin fansar naira miliyan 30, bayan sun tafi da yarsa mai shekaru 20.

Bayan samun korafin ne kwamishinan yan sandan jahar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya tashi dakarun yan sandan dake yaki da ma su garkuwa da mutane karkashin jagorancin SP Aliyu Muhammed Auwal, tare da basu umrnin kubutar da ita su kuma tabbatar da sun kamo wadanda ake zargin.

Idongari.ng, ta ruwaito cewa, jamiā€™an yan sandan sun yi nasarar kubutar da Hafsat Nuhu, bayan ta yi kwanaki 37 a maboyar ma su garkuwa da mutanen da ke cikin dajin Gubuchi a karamar hukumar Makarfi ta jahar Kaduna.

Haka zalika dakarun sun kubutar da wani mai suna Alhaji Badaru Adamu, mai shekaru 65 , mazaunin Mahuta a karamar hukumar Kubau ta jahar Kaduna, da shima ma su garkuwar suke rike da shi tsawon mako guda.

An kama wadanda ake zargin a cikin dajin, da suka hada Yakubu Abubakar mai shekaru 40 da kuma Ali Noti mai shekaru 50 .

Mutanen da yan sandan suka kubutar sun bayyana cewa ruwan lemo da Burodi suke ba su, sai kuma dukansu da suke yi, tare da daure su da kacar babur.

Rundunar yan sandan ta ce yanzu haka batun yana sashin gudanar da binciken manyan laifuka kuma da zarar ta kammala bincike za a gurfanar da su a gaban kotu don su fuskanci hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *