A yau ake sa ran babbar kotun tarayya a Najeriya za ta sanya rana domin fara sauraron wata ƙara da wani lauya mai rajin kare haƙƙin ɗan’adam ya shigar inda yake ƙalubalantar matakin kama mabarata a Abuja, babban birnin ƙasar.
A makwannin baya ne, ministan Abuja Mista Nyesom Wike ya ƙaddamar da matakin kama mabarata waɗanda ya ce sun cika titunan Abuja, har ma sun zama barazana ga tsaron birnin, kuma suna zubar da mutuncin Nijeriya a idon baƙi da ke zuwa kasar.
Sai dai, Barrista Abba Hikima, wanda ya shigar da ƙarar ya ce matakin ya saɓa wa tsarin mulkin Nijeriya, inda ya ce yanayin ƙasar ce ta jefa mutane halin da suke ciki.