An mayar da Muhammadu Sanusi II kan muƙamin sarkin Kano

Spread the love

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sanar da mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano.

Gwamna ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan sanya hannu kan dokar da ta yi gyara ga dokar da ta kafa dokar masarautun Kano ta 2019.

A yau Alhamis ne Majalisar dokokin ta jihar Kano ta yi wa ƙudurin dokar soke masarautu biyar na Kano – wato Kano, Bichi, Rano, Karaye da Gaya karatu na uku tare da amincewa da ita.

Daga nan ne aka miƙa dokar ga gwamnan wanda ya sanya mata hannu.

A lokacin jawabin da ya yi, Gwamna Kabir ya ce: “Bayan soke dokar masarautu ta jihar Kano ta 2019, hakan na nufin cewa masarautar Kano ta koma matsayinta gabanin dokar ta 2019”.

Ya ƙara da cewa “hakan na nufin babu wani halastaccen sarki a Kano face Sarki Muhammadu Sanusi”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *